Tsohon mai tsaron ragar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Flying Eagles John Falegha ya rasu.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya (NFF) ta ce John Falegha ya rasu ne a ranar Lahadi 30 ga watan Agustan 2020 a ƙasar Senegal.
Falengha golan ‘yan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya ‘yan ƙasa da shekaru 17 da ‘yan ƙasa da shekaru 20 ya rasu yana mai shekaru 26.
Hukumar ta NFF ta aike da saƙon ta’aziyar rasuwarsa ga iyalansa ta kafar sadarwa ta Twitter a ranar Litinin.
Mutane da dama a faɗin ƙasar nan dama ƙasashen ƙetare na ci gaba da nuna jajensu dangane da rasuwar mai tsaron ragar.