Tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Cif Luka Barau Dameshi, ya yi murabus na zama memba a jam’iyyar adawa ta PDP, inda Kuma ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Idan za’a iya tuna wa dai, Dameshi ya bar APC Mai Mulki tun a shekarar 2014 zuwa PDP, inda Kuma a yanzu ya bayyana matsayar sa, a cikin wata wasika mai kwanan wata 13 ga Satumba, 202, kuma ya aika zuwa ga shugaban jam’iyyar a mazabarsa dake karamar hukumar ta Ningo/Boher, na karamar hukumar Akwanga a jihar.
Sai dai jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa, ko da ta nemi sanin dalilin ficewarsa daga PDP zuwa APC a yanzu, ya amsa mata ta sakon kartakkwana cewa, “Tabbas na sauya sheka, kuma shawara ce ta kashin kai.”
Dameshi ya zama mataimakin gwamna a lokacin mulkin farko na Gwamna Umaru Tanko Al-Makura, daga shekarar 2011 zuwa shekarar 2015.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane 11 sun mutu a hadarin mota a Osun
A wani labarin Kuma na daban
Jami’an Rundunar yan sanda a Jigawa sun cafke wani mutum mai shekaru 25, bisa zargin shi da yin lalata da akuya a karamar hukumar Gwaram dake jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Jigawa, ASP Lawan Shiisu ne, ya tabbatar da kamun wanda ake zargin, a cikin wata sanarwa da ya fitar a a garin Dutse Babban Birnin jihar a yau Juma’a.
Shiisu ya ce, jami’an Yan sanda sunyi nasaran kama wanda ake zargin ne, da misalin karfe 1 na safe, yayin da jami’an rundunar ke sintiri a cikin garin Gwaram.
Ya bayyana cewa wanda ake zargin, mazaunin unguwar Kunnadi ne, yayin da jami’an rundunar dake sintiri a yankin suka cafke shi, yana jima’i da akuya.
“Da misalin karfe 0100 na safe, ‘yan sanda daga Shelkwatar Runduna ta Gwaram, yayin da suke sintiri a cikin garin Gwaram da kewayenta, sun cafke wani matashi dan shekara 25 mazaunin unguwar Kunnadi, yayin da yake saduwa da akuya,” inji Shiisu a cikin sanarwar.
Kazalika Kakakin ya kara da cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin, sannan idan an kammala za’a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu domin ya girbi abun da ya shuka.