Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi kira ga shugabannin siyasa da na gargajiya da na addini da su hada kai wajen ganin an warware matsalar rashin tsaro da kasar ke fama da ita.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya damu musamman da tabarbarewar tsaro a fadin kasar musamman a arewacin Najeriya.
Mista Abubakar ya ce ya je Sokoto ne domin jajantawa gwamnan jihar bisa rasuwar babban yayansa da kuma jajantawa al’ummar jihar Sokoto da ma yankin arewa maso yamma bisa karuwar kalubalen tsaro a yankin siyasar kasar.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana matsalar tsaro a arewacin Najeriya a matsayin abun takaici, ya kuma koka kan yadda ta’addancin da ake tafkawa a yankin.
Ya ce Arewacin Najeriya da aka san shi da zaman lafiya ya fada cikin rudani da ba zai ba da damar cigaba mai ma’ana a yankin ba.
Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya ce sauran yankunan da ke yankin siyasar Arewacin Najeriya na fuskantar kalubalen tsaro tun daga rikicin kabilanci zuwa ayyukan ta’addanci da ‘yan fashin daji.
Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su kara kaimi wajen addu’o’in Allah ya kawo mana karshen matsalar tsaro.
Ya kuma jajanta wa Gwamna Tambuwal bisa rasuwar babban yayansa da kuma yawan mace-mace da barna da kalubalen tsaro ke fuskanta a jihar.
Haka kuma a Sokoto domin ta’aziyyar akwai shugaban majalisar dattawan Najeriya wanda ya mika sakon ta’aziyyar majalisar ga gwamnan bisa rasuwar yayansa.
Shugaban majalisar dattawan ya je Sokoto ne tare da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni inda suka yi addu’ar Allah ya jikan marigayin.