Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da Kisan Yaro dan kimanin shekara bakwai da haihuwa da wasu mutane suka yi a Kaduna.
Idan za a iya tunawa dai kwanaki biyu kenan da labarin kisan yaron ya buwayi gari, bayan garkuwa da shi da wasu matasa suka yi a Kaduna.
Daya daga Jagoran masu garkuwa da yaron wanda tsohon Sojan Najeriya ne, mai suna SA Galadima, ya bayyana cewa sun dauki matakin kashe yaron ne duk da cewa an biya su kudin fansa naira miliyan biyar da suka gabata don gudun kada ya tona musu asiri.
A sakon da ya wallafa a shafin sa na Facebook, Alhaji Atiku Abubakar ya ce ya yi matukar kaduwa tare da bakin cikin jin wannan mummunar labari.
Ya kara da cewa bai kamata a zura idanu abubuwa makamantan Wannan na ci gaba da faruwa a kasar nan ba, don haka akwai bukatar kasar nan ta rungumi tsarin dan sanda na al’umma wato Community Policing.
Kalaman sa “Na yi mutukar bakinci da jin labarin sace matashin nan Ahmad Kabir, wanda daga bisani aka tsinci gawar sa a cikin magudanar ruwa, bayan iyayen sa sun biya kudin fansa Naira miliyan biyar”
“Ba zai yuwu mu ci gaba da rayuwa haka ba, Wajibi ne Najeriya ta rungumi tsarin aikin ‘dan sanda na al’umma, wanda zai dace da muradun “Yan kasa, domin magance matsalar rashin tsaro”
Yanzu haka dai SA Galadima na chan tsare a hannun yan sanda, yayin da ake ci gaa da neman abokan cin mushen sa ruwa a jallo.