Tsohon ministan wasanni da ci gaban matasa, Solomon Dalung, ya yi murabus daga jam’iyyar APC.
Dalung, wanda ya rike mukamin minista a wa’adin farko na shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar ta hanyar wata wasika mai dauke da kwanan watan 18 ga Afrilu, 2022.
A cikin wasikar da ya aike wa shugaban gundumar Sabongida a karamar hukumar Langtang ta Kudu a jihar Filato, tsohon ministan ya dora matakin da ya dauka kan “rashin wanzar da dimokuradiyyar cikin gida” a jam’iyya mai mulki.
Wasikar ta ce, “inaso in bayyana ficewana daga jam’iyyar APC daga ranar da aka bayar da sanarwar.
“Yana da kyau a ambaci cewa abubuwan da ke faruwa a cikin jam’iyyar a baya-bayan nan sun ci karo da ainihin ka’idoji da kimar da ke tattare da tushen jam’iyya. Abin lura shi ne cewa dimokuradiyyar cikin gida na da matukar muhimmanci ga dorewar dimokuradiyyar yayan jam’iyar, wanda ya zama abin al’ajabi.”
Lalong dai yana sukar gwamnatin Buhari a ‘yan kwanakin nan, kafin daga fisani ya bayyana ficewarsa.
Awani labari Kuma na daban.
Ko Matar Buhari bata Amince da Tsare-tsaren shi — Kukah ya maidawa Fadar Shugaban Ƙasa Martani
Shugaban Cocin Katolika dake Sokoto Matthew Kukah yace Aisha Buhari, Uwargidan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta amince da abinda ya faɗa akan Mijin ta.
Kukah ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa da Gidan Talabijin na Arise TV a ranar Talata da safe, wanda Majiyar Wakilin mu ya shaida.
Bishop a lokacin da yake sanar da hujjojin sa, yace baya da wani abu tsakanin sa da Shugaban Ƙasa, amma akwai wasu Tsare-tsare da Aisha bata amince dasu ba.
Kukah yace “dukkanin waɗanda suke cewa ina caccakar Shugaban Ƙasa, ban taɓa caccakar shi ba. Dukkanin abinda nake cewa shine bashi iya Dai-dai to na Ƙasa.
A cewar sa yana da girmama Shugaban Ƙasa, kuma yana kallon shi a matsayin sa na Dattijo, amma idan ya kalle shi a matsayin Shugaban Ƙasa, sai yaga ya kasa kwata-kwata na yin aikin sa.
Comments 1