Tsohon Ministan Buhari ya buƙaci Kotu ta haramtawa Tinubu, Atiku Takarar Shugabancin Ƙasa
Tsohon Ƙaramin Ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba da wata kungiya mai suna Incorporated Trustees of Rights for All International, sun shigar da ƙara a gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja suna neman ta bada umarnin da zai ayyana Nwajiuba a matsayin sahihin ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC.
Masu shigar da ƙara na kuma son a soke ƙuri’un da ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu suka samu; da kuma jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mota ta murkushe ‘yan Okada 3 har lahira a Ogun
Wadanda ake kara na farko zuwa na shida a karar mai lamba FHC/ABJ/CS/942/22 sune: APC, PDP, Tinubu, Atiku, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya da kuma Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta.
Nwajiuba, wanda shima ya sayi fom din Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC a kan Naira miliyan 100, amma ya samu kuri’a ɗaya kacal a zaɓen fidda gwani na ranar 8 ga watan Yuni, inda ya zargi Tinubu da cin hancin delegates da Daloli.
Masu shigar da karar sun kuma danganta a matsayin shaida wani faifan bidiyo da ke nuna tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, yana ƙorafin cewa wakilan da suka fito zaben fidda gwani na APC sun sayar da kuri’unsu.
“Wadanda suka kaɗa ƙuri’a a zaben fidda gwani na APC, su waye? Su talakawa ne ƴan Najeriya. Kuɗaɗen da suka samu sun warware musu matsalar nan take, yanzu suna cewa sun yi kuskure; yanzu kuna jin abubuwa daban-daban da suke faɗa,” in ji Amaechi a wajen bikin cika shekaru 60 na Apostle Eugene Ogu, Janar Babban mai kula da Ofishin Jakadancin Abundant Life Evangel, a makon jiya.
Bisa ga shaidar, Nwajiuba da Ƙungiyar RAI sun gabatar da batutuwa 25 don yanke hukunci daga kotu.
Musamman Tsohon Ministan ya bukaci Kotun da ta tantance ko adadin wakilan ya ci karo da sashe na 11 (A) 12(1) da 13(1) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC.
Tsohon ministan ya kuma bukaci kotun da ta tantance ko adadin wakilan da za a yi zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP ya sabawa sashe na 33(1) da (5) (c) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Masu gabatar da kara sun buƙaci Kotun da ta dubacikakken bayani dalla-dalla da tanade-tanade na Sashe na 6 (6) (A) (B) da (C) da aka karanta tare da sashe na 15 (5) na Kundin Tsarin Mulki na 1999, kotun nada iko sokewa, sokewa da ayyan haramtattun zabukan fidda gwani na shugaban kasa na APC da PDP.
Nwajiuba ya roki kotun da ta tantance duk kuri’un da aka kada wa Tinubu da Atiku a babban taron ƙasa musamman na jam’iyyun APC da PDP sun sabawa doka, kuma ba su da wani tasiri a kan almundahana da sayar da kuri’u da masu kada kuri’a suka yi.
A karshe, tsohon ministan ya roki kotun da ta yanke hukunci game da tanadin sakin layi na 1 da na 8 na jaddawali na 5 na kundin tsarin mulkin 1999, cin hanci da rashawa na “wanda ake kara na uku (Tinubu) da wanda ake kara na 4 (Atiku) wajen sayen kuri’u da cin hanci da rashawa da cusa wa wakilai daloli da Naira domin su samu kuri’u a babban taron ƙasa.
Saboda haka, tsohon Ministan yana neman sauyi har guda 26 ciki har da umarnin cewa ba a tsara adadin wakilai a APC da PDP yadda ya kamata ba.
Musamman Nwajiuba ya roki kotun da ta yanke hukuncin cewa Atiku da Tinubu tare da wakilansu sun baiwa wakilai cin hancin daloli sannan a bayyana kuri’un da suka samu a matsayin haramtacce.