Tsohon Ministan harkokin noma a Nigeria Dakta Malami Buwai ya riga mu gidan gaskiya sakamakon doguwar jinya da ya yi ta fama da ita.
Dakta Malami wanda ya yi ministan harkokin noma a shekarar 1994 karkashin mulkin tsohon shugaban ƙasa Janar Sani Abacha, ya rasu ne a yammacin ranar Litinin a mahaifarsa ta Gusau dake zama fadar gwamnatin jihar Zamfara.