Tsohon Ministan Sufuri Ibrahim Isa Bio ya canja sheƙa daga Jam’iyyar APC zuwa PDP a ranar Alhamis.
Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jahar Kwara ya canja jam’iyyar tare da magoya bayan sa, a mazaɓar sa ta Gure/Gwasoro ta Ƙaramar Hukumar Baruten ta Jahar Kwara.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a Ilori, inda Sakataren Jam’iyar PDP a Jahar Kwara Tunde Ashaolu, ya taya Bio murnar shigowa Jam’iyyar, yana mai yaba masa akan ɗaukar matakin daya kamata na shiga jam’iyyar.

KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben Gwamna: An aike da Dakarun Civil Defence 20,000 Jihar Anambra
Yace “abunda yayi, yayi dai-dai da buƙatar ƴan Kwara wanda suka gaji da yanda Gwamnatin Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ke mulkar jahar. Muna kuma taya Tsohon Ministan Sufuri Ibrahim Isa Bio da masoyan sa murna zuwa jam’iyyar PDP.
Ashaolu ya bayyana fatan cewa canza jam’iyyar sa zai inganta harkokin jam’iyyar, ta la’akari da yanda ake girma mashi, kuma ɗan siyasa mai jajirtacce.