Tsohon Sakataren Harkokin tsaron Amurka Donald Rumsfeld wanda ke ɗaya daga cikin mayakan da suka fafata yaki a kasar Iraqi ya rigaye mu gidan gaskiya.
Donald Rumsfeld wanda ya yi aiki karkashin tsohon shugaban kasa George W. Bush, shine Kwamandar da ya jagoranci yaki da yan ta’adda na kasar.
A shekara ta 2003 ne dai Amurka ta kaddamar da wani shiri a kasar Afghanistan bayan harin sha daya ga watan Satumba, inda Amurkar ta mamaye Kasar ta Iraki.
Sai bayan wani tawaye da aka yi wa dakarun sojin Amurkar a shekara ta 2006, ya sa Mista Rumsfeld ya yi murabus duk da cewa ya kare tarihinsa na gwarzon yaki.
Mista Rumsfeld ya mutu ne a kauyensa na Taos dake Jihar New Mexico.