Abdelaziz Bouteflika, wanda ya mulki Algeria na tsawon shekaru 20 kafin ya yi murabus a shekarar 2019, yayin da manyan zanga -zanga suka mamaye kasar, ya mutu.
Bouteflika ya mutu ranar da ta gabata Juma’a yana da shekaru 84 a duniya.
Tsohon mai rike da karfin ikon mulkin kasar Algeria, ya bar ofishin sa ne a watan Afrilun shekarar 2019, sakamakon matsin lamba daga rundunar sojin Kasar, biyo bayan barkewar mummunar zanga -zangar da aka kwashe makwanni a nayi a kasar, kan yunkurinsa na yin tazarce a wa’adi na biyar.
Bayan ya yi murabus, ya kasance ba ya bayyana a gaban jama’ar kasar inda ya boye Kansas a wani gida dake yammacin yankin Algiers dake kasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu wakoki ne suke rike da Kannywood ba fim ba, inji Aminu S Bono
Bouteflika ya zama Shugaban Algeria ne a shekarar 1999, yayin da tsohon mulkin mallaka na Faransa ya Sami cikas bayan kwashe shekaru goma a na yakin basasa a kasar, wanda ya lakume rayukar mutane kusan 200,000 a Algeria.
Al’umar kasar sun yi wa Marigayin lakabi da “Boutef”, Wanda tun farkon Mulkin sa, ya sami kyautar girmamawa kan yunkurin shi na taimakawa wajan samar da zaman lafiya a kasar, ta hanyar Samar da dokar afuwa, wacce ta sa dubunnan mayaƙan Islama mika wuya, tare da bada makamansu.
A wani labarin na daban.
Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta sallami jami’anta guda biyu, saboda cin zarafin wani farar hula.
Kakakin rundunar, DSP Bright Edafe, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa daya rabawa manema labarai ranar Juma’a a Warri.ya kara da cewa wadanda aka sallama sun hadar da Felix Ebikabowei da sajen Ndubuisi Abazie,sannan yace har kawo wannan lokacin da aka sallame su, suna hade da sashen ‘B’, na Warri.
A cewarsa, Kwamishinan ‘yan sanda CP a jihar, Mista Ari Ali ya kuma umarci’ yan sandan da aka kora da aci gaba da tsaresu a sashin binciken manyan laifuka na jihar.inda ya kara da cewa za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike. , bayan rufe aiki, jami’an sun yi shawara kuma sun shiga aikin ba bisa ƙa’ida ba a kan shataletalen Titin Estate dake Warri.
“Sun kama wani mahayan babur mai kafa uku guda daya mai suna Omesan, bayanda Rikici ya shiga tsakaninsu da ‘yan sandan da wanda aka kashe kuma ana zargin sun tura shi da duka wanda hakan ya kai ga samun munanan raunuka a kansa.
“Nan take CP ya ba da umurnin a mika shari’ar zuwa sashin binciken manyan laifuka na Jiha domin gudanar da bincike cikin hikima da nuna son kai.” Daga baya bincike ya nuna cewa jami’an biyu suna da karar da za su amsa a kan munanan hare haren da aka kaiwa wanda har yanzu yana cikin mawuyacin hali.
“Bijirewa umurnin doka wanda ya saba da sakin layi na E (iii) jadawalin farko na Dokar‘ Yan Sanda da Dokokin 370, sakin layi na F na Dokar ‘Yan sanda da Dokokin CAP P.9 na Tarayyar Najeriya na shekarar 2004.
Yace Kwamishinan ya gargadi jami’an rundunar kan cin zarafin bil adama, rashin sanin yakamata ga membobin jama’a da kuma rashin sanin yakamata a dukkan fannoni.