Tsohon shugaban kasa,, kuma jami’in da ke shiga tsakani a kasar Mali Dr Goodluck Ebele Jonathan ya isa birinin Bamako sakamakon yadda ake samun shakku game da mika mulki zuwa hannun fararen hula da gwamnatin rikon kwaryar kasar ta yi alkawari.
Tun bayan da sojojin kasar karkashin jagorancin Assimi Goita suka gudanar da juyin mulkin a watan Agusta, suka yi alkawarin mika mulki hannun farar hula a watan Fabrairu mai zuwa.
To sai dai an fara samun shakku game da hakan, la’akari da yadda har ya zuwa yanzu sojojin suka yi shiru game da fara shirye-shiryen mika mulkin, abin da ya fara jefa shakku a zukatan jama’a.
Ana sa ran Gooodluck zai tattauna da kwamitin shirya zabe na gwamnatin rikon kwaryar ta Mali, kungiyoyin al’umma da kuma jam’iyyun siyasa.
An dai shirya cewa, Goodluck zai fara ganawa da Firaminista Choguel Maiga, yayin da daga bisani kuma ya gana da shugaban gwamnatin Assimi Goita a yau Talata.
Tun bayan juyin mulkin, sojoji sun yi alkawarin shirya zaben ‘yan majalisa da na kananan hukumomi a ranar 26 ga watan Disamba, sannan kuma a gudanar da na shugaban kasa a ranar 27 ga watan Fabrairun badi.
To amma shirun da sojojin suka yi game da fara shirye-shirye ya sanya aka fara fargaba game da cewa, ko suna son yin kaka-gida a mulkin Malin ne.