By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gana da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a fadar sa ta Villa dake Abuja ranar Alhamis.
Jonathan wanda ya isa fadar Villa da misalin karfe uku na rana, ya shiga ganawar sirri da shugaban kasar nan take.
Sai dai kuma fadar ta shugaban kasa bata bayyana ajandar taron da suka tattauna ba.
Kazalika an samu labarin cewa za a iya danganta hakan da aikin Jonathan a matsayin manzon musamman na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka a Mali inda yake jagorantar tattaunawar sasantawa yayin da kasar ke ci gaba da zama karkashin mulkin soja bayan juyin mulkin da aka yi a watan Agustan 2020 wanda ya hambarar da tsohon shugaban kasar Ibrahim Keita.
A ranar litinin da ta gabata ce gwamnatin kasar Mali dake karkashin mulkin soja ta kaddamar da wani taron kasa na kwanaki hudu kan maido da kasar ga mulkin farar hula.