Tsohon shugaban kasar Koriya ta Kudu Chun Doo-hwan, wanda ya kafa mulkinsa bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 1979 Wanda hakan ya haifar da gagarumar zanga-zangar dawo da demokuradiyya a kasar, ya rasu a ranar Talata yana da shekaru 90 a duniya.
Chun yana da ciwon daji na jini wanda kuma rashin lafiyarshi tayi kamari a kwanan nan, in ji tsohon sakataren yada labaransa Min Chung-ki ga manema labarai.
Ya rasu ne a gidansa da ke birnin Seoul da sanyin safiyar Talata kuma za a mika gawarsa domin yi masa jana’iza a yau.
Idan za’a iya tunawa Wani tsohon kwamandan soji, Chun ne ya jagoranci kisan kiyashin da sojojin Gwangju suka yi a shekarar 1980 ga masu zanga-zangar neman dawo da mulkin dimokradiyya a kasar, wanda daga baya aka yanke masa hukuncin kisa.
An haifi Chun a ranar 6 ga Maris, 1931, a Yulgok-myeon, wani gari mai fama da talauci a lardin Hapcheon da ke kudu maso gabashin kasar, a lokacin mulkin mallakan da Japan tayiwa Koriya.
Da yake jagorantar binciken kisan shugaba Park Chung-hee a waccan shekarar, Chun ya kai karar manyan abokan kawancen soji tare da samun iko da hukumomin leken asirin Koriya ta Kudu inda ya buga labarin juyin mulkin a ranar 12 ga watan Disamban.
Ya shiga aikin soja kai tsaye daga makarantar sakandire, inda ya yi aiki har zuwa lokacin da aka nada shi kwamanda a shekarar 1979.