By Abbas Yakubu Yaura
Wani tsohon shugaban kungiyar dalibai a kwalejin fasaha ta jihar Osun, Iree, Bolaji Olaniyi, ya zargi mahukuntan makarantar da hana shi sakamakon karatun sa da gangan.
Olaniyi, a cikin wata sanarwa da ya samu a Osogbo, yace lamarin ya fara ne tun a shekarar 2019, biyo bayan wata zanga-zanga da ya yi bayan wani dalibin makarantar, Hammed Sheu, ya fadi a daki jarabawar, inda kuma aka garzaya da shi asibitin koyarwa na kwalejin, amma mahukuntan asibitin suka gaza zuwa gare shi.
Ya ce daga baya dalibin ya mutu yayin da aka garzaya da shi wani asibiti da ke wajen harabar kwalejin fasahar.
“Wannan ya sanar da zaluncin dalibi, daya kai ga hankalin shugaban cewa, wasu dalibai na hada kansu domin yin wata mummunar zanga-zanga a cikin babbar harabar makarantar a washegari.
“Shugabannin daliban karkashin jagorancin Kwamared Bolaji Olaniyi, a kokarin da suke na dakile faruwar lamarin da kuma tabbatar da cewa daliban ba su karkata ba, sun yi garkuwa da muzaharar tare da kiran wata zanga-zangar a kofar makarantar maimakon cikin harabar makarantar.
“Yayin da shugaban ke jawabi ga daliban a kofar makarantar, wasu ‘yan ta’addan sun hada kansu ta hanyar kofar shiga daban-daban domin lalata asibitin makarantar, hakan ya sa hukumar makarantar ta dakatar da shugaban daliban na tsawon zangon karatu biyu.
“Tun daga lokacin da dakatarwar ta wuce a shekarar 2021, amma har yanzu makarantar ba ta fitar da sakamakonsa ba. Shugaban daliban ya ziyarci harabar jami’ar a lokuta da dama, inda ya zagaya Legas zuwa Osun, domin warware matsalar a makaranta, amma labari daya ne a koda yaushe kamar yadda aka ce ya samu sabani a cikin suna,” inji shi.
A cewarsa, duk takardun da ake bukata an mika wa makarantar a lokacin da ake shirin shiga makarantar, amma hukumar ta yi ikirarin cewa babu takardun.
Ya kara da cewa, duk da an fahimci cewa an kulla makarkashiya, amma har yanzu ya mika dukkan takardun da aka bukaci a daidaita kura-kuran, kuma bayan shekara guda ba a shawo kan matsalolin ba, saboda har yanzu sakamakonsa na hannun hukumar makarantar.
Da yake mayar da martani kan zargin a ranar Litinin, jami’in hulda da jama’a na kwalejin, Mista Tope Abiola, ya tabbatar da cewa an hana sakamakon dalibin.
Sai dai ya ce ba a fitar da sakamakon ba ne saboda sabanin sunayen da tsohon shugaban kungiyar SUG ya yi wa rajista, amma ya tabbatar da cewa za a fitar da sakamakon bayan an magance sabanin.
Abiola ya ce, “ya kammala karatunsa ne da sunaye, daban da wanda ke cikin sakamakon sa na ND. Shi ne ya jinkirta tafiyar da lamarin, amma duk da haka, ya yi abin da muka ba shi shawarar ya yi.
Muna aiki a kai, don aiwatarwa da kuma fitar da sakamakonsa. Za a yi a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa kuma zai sami sakamakonsa.
“Ba wai da gangan muka jinkirta shi ba. Ya ci karo da dakatarwar da aka yi masa, amma ba za mu iya ba shi satifiket kawai ba sai an magance kura-kuran da aka yi da sunansa.”