Tsohon shugaban majalisar Dattawa ta kasa, David Bonaventure Mark a ranar Talata ya kaddamar da ginin tituna guda uku a karkara a jihar Bauchi.
Da yake magana a wurin taron kaddamar da titunan wanda tsawonsu ya kai kilomita 35.5 wanda ya hada da Warji – Gwaram, Bogoro-Lusa da kuma Boi-Tapship, Mark ya ce bude wadannan hanyoyi zai kawo ci gaba ga al’ummar da suke yankin.
Taron dai ya gudana ne a Katanga Warji. Tsohon shugaban majalisar Dattawan Nijeriyar, ya jinjinawa gwamna Bala Mohammed Abdulkadir bisa wannan aiki da ya dora aniyar yin a tituna a karkara, wanda ya shawarce shi da ya yi aiki tukuru wajen gina yankunan karkara domin kawo ci gaba.
A na shi jawabin, Gwamna Bala ya ce gina titunan nan suna da matukar muhimmanci wajen kawo ci gaba, domin a cewar shi, samun kyakkyawan hanya dama ce ta kyakkyawan shugabanci, wanda ya ce gwamnatinsa za ta maida hankali wajen yin sabbin tituna a jihar.