Tsohon shugaban matasar jam’iyyar PDP mai adawa kasar nan Dennis Alonge ya tattara nasa-inasa tare da dumbin magoya bayansa izuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Mista Dennis Alonge wanda ya sanar da wannan sauyin sheka tasa a sakatariyar jam’iyar PDP dake Akure na jihar Ondo, ya bada tabbacin taimakawa APC ta kai ga gaci.
Kazalika shi ma wani tsohon shugaban karamar hukuma a jihar mai suna Akin Aibunuomo ya tattara komatsonsa tare da magoya bayansa inda ya jibge a jam’iyyar tsintsiya ta APC.
Da yake tarbarsu, gwamnan jihar Ondo Mista Rotimi Akeredelu ya babu shakku za a sanya dukkanin su cikin aikace-aikace da shirye-shiryen jam’iyyar, kuma za a kare musu martabar su.
Tun farko jagoran tawagar masu sauya shekar, Dennis Alonge ya ce aikace aikacen raya al’umma na gwamnan jihar ne ya ja hankalin su zuwa jam’iyyar ta APC.