Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya tafi birnin Nairobi na kasar Kenya, inda zai jagoranci tawagar masu sa ido a babban zaben kasar.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa an shirya gudanar.da zaben ne a ranar 9 ga watan Agustan 2022.
Jonathan zai yi aiki a matsayin shugaban tawagar sa ido kan zabe na cibiyar zabe don dorewar dimokuradiyya a Afirka, wadda ta tura tawagar masu sa ido na gajeren zango zuwa Kenya.
A cewar wata sanarwa da EISA ta fitar a birnin Nairobi, tawagar ta kunshi masu sa ido na 21, wadanda akasarinsu sun fito ne daga kungiyoyin farar hula, kungiyoyin gudanar da zabe da kuma masana daga sassan nahiyar.
Sanarwar ta ruwaito Jonathan ya bayyana cewa, “za’a tura masu sa ido a dukkan yankuna, musamman a yankuna kasar 10, inda za su lura da matakin karshe na yakin neman zaben jam’iyyun siyasa, da tsarin ranar zabe da kuma sakamakon gudanar da taro.”
Ta kara da cewa tawagar sa ido kan zaben EISA za ta fitar da sanarwa ta farko kan sakamakon bincikenta a wani taron manema labarai da zata gudanar a ranar 11 ga Agusta 2022.