Rahotanni sun tabbatar da rasuwar tsohon Shugaban NNPC, Dakta Maikanti Baru da sanyin safiyar yau Asabar 30 ga watan Mayun 2020.
Babu wani takamaimen bayanin dalilain rasuwarsa, sai dai wadansu majiya sun tabbatar mana da cewa an kwantar da shi a asibitin Cedarcrest dake birnin tarayya Abuja.
Ya zuwa yanzu ana sa ran gudanar da jana’izarsa ba da jimawa ba a garin na Abuja.