By Abbas Yakubu Yaura
Tsohon Mataimakin Shugaban Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna Farfesa Mohammed Abubakar Daniya ya rasu, ya yana da shekaru 72 aduniya a daren Juma’a a Minna, bayan gajeruwar rashin lafiya.
Farfesa Daniya ya taba zama shugaban jami’ar tarayya, Bida kuma mataimakin shugaban jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida dake Lapai a jihar Neja.
A cikin sakon ta’aziyyar Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya bayyana marigayi Farfesa a fannin kimiyyar lissafi a matsayin fitaccen malami, wanda ake mutuntawa, wanda ya bayar da gudunmawa sosai wajen bunkasa ilimi a jihar da kasa baki daya.
Ya ce jihar ta yi hasarar daya daga cikin masu bin diddigin ilimi, hazikan malami da gudanar da jami’o’in da ayyukansu na rayuwa da basirarsu ke da kishi kuma za su kasance maras kima a tarihin jihar.
“Mun yi baƙin ciki. Babban rashi ne mai raɗaɗi kuma maras musanyawa ga jiha da ƙasa baki daya.
“Marigayi Farfesa Daniya mutum ne mai cikakken gaskiya da da’a wanda ya yi kokarin ganin ya samu nagarta da kuma kare muradun manyan makarantun da ya jagoranta a matsayin mataimakin shugaban jami’ar da kuma shugaban Kwaleji,” in ji Gwamna Bello.
Gwamna Bello ya ce tsohon malamin jami’ar za a yi kewar sa sosai saboda hazakarsa na gudanar da mulki, musamman a lokacin da ya ke shugabantar Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Bida; Mataimakin Shugaban Jami’ar Fasaha ta Tarayya, (FUT) Minna da Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida, (IBBUL) Lapai da kuma Shugaban Majalisar Gudanarwa na Kwalejin Ilimi ta Jihar (COE), dake Minna.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya baiwa iyalansa hakurin jure wannan rashi, ya kuma jikansa da rahama ya kuma saka shi a gidan Aljannah Firdausi.
Kazalika Marigayin an nada shi shugaban kwalejin fasaha ta tarayya dake Bida daga shekarar (1991-1997) kuma ya zama mataimakin shugaban jami’ar FUT MINNA na uku daga shekarar (1997-2002).
Sannan ya kuma taba zama Mataimakin Shugaban Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBUL), dake Lapai.
Kafin rasuwar sa an nada shi Shugaban Hukumar Gudanarwa na Kwalejin Ilimi ta Jihar (COE) dake Minna daga shekarar 2012-2016, sannan kuma Farfesa mai ziyara a Hukumar Jami’ar Kasa (NUC).
Marigayin an haife shi a ranar 15 ga watan Yunin shekarar 1950, a Bida ta Jihar Neja, Marigayi Farfesa Daniya ya kasance mai kula da jami’a, malami kuma mai bincike wanda ya taka rawa wajen tsara muhimman tsare-tsare don ceto ilimin kimiyya da fasaha a kasar.