By Abbas Yakubu Yaura
Amina Uba Hassan, tsohuwar matar fitaccen jarumin Kannywood, Adam A Zango, ta dawo harkar fim a hukumance a matsayin babbar jaruma.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Amina wacce aka fi sani da Maman Haidar ta fara zama jaruma a Kannywood a farkon shekarun 2000 amma ta auri Zango a shekarar 2007.
Sai dai jarumar ta haifi da namiji a shekarar 2008 kuma auren nata ya samu tan garda bayan watanni biyar.
Bayan auren da ya yi rashin nasara, jarumar ta ci gaba da zama, sai dai ta sake fitowa a wani shiri na gidan talabijin na ‘Gidan Danja’ wanda kamfanin 2Effects ya shirya a kwanakin baya.
Kazalika Jarumar wacce haifaffiyar Kaduna ce tace ta dawo masana’antar fiye da yadda ta bari, kuma a wannan karon, sararin sama ne iyakarta.
Masoya sun yi ta yabawa rawar data taka a shirin da ake yadawa a tashar Arewa24.