Hukumar tsaron Farin Kaya ta DSS ta sako tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Obadiah Mailafia, bayan ya sake amsa gayyatarta a karo na biyu.
Dakta Mailafia, wanda kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar nan ne a zaɓen shekara ta 2019 a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, ya je ofishin hukumar ne da ke Jos da misalin ƙarfe 12 na rana, daga bisani kuma aka sallame shi sa’a ɗaya bayan zuwan nasa.
Da safiyar Litinin ne dai hukumar ta sake gayyatarsa domin ya amsa tambayoyi a karo na biyu, kamar yadda lauyansa, Yakubu Bawa, ya tabbatar wa Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN).
Lauyan ya kuma ce sabuwar gayyatar na da nasaba da ganawar Mailafia da hukumar a makon jiya.
“Ba wani abu ba ne na daban da ganawarsa ta farko da DSS, wadda ta musayar ra’ayi ce kawai”, inji shi.
https://dimokuradiyya.com.ng/ya-kamata-a-hukunta-mailafiya-shugabannin-arewa/
Idan ba a manta ba, ranar Larabar makon jda ya gabata me hukumar DSS ta gayyaci Mailafia bayan wata tattanawa da ya yi da gidan rediyon Nigeria Info da ke Abuja.
Yayin tattaunawar dai Mailafia ya yi zargin cewa ɗaya daga cikin gwamnonin arewa na mara wa Boko Haram.
Daga bisani hukumar ta saki tsohon Mataimakin Gwamnan na CBN bayan an kwashe sa’o’i shida ana yi masa tambayoyi.
Hukumar dai ta fitar da sanarwa tana cewa Dakta Mailafia ya yi nadamar abubuwan da ya faɗa har ya nemi afuwa, shi kuma ya ce yana nan a kan bakanshi.