Wasu tubabbun Yan bindiga da suka fito da sassan daban-daban na jihar Cross River suka toshe ofishin gwamna Ben Ayade na jihar
Sun hana jami’an gwamnati da masu rike da mukaman siyasa da manyan ma’aikatan gwamnati da ba su shiga yajin aikin kungiyar NLC shiga ofisoshinsu.
Daya daga cikin masu magana da yawunsu ya ce: “Tun da suka roke mu, muka bi abun da sukeso, muka yi watsi da ayyukanmu muka mika bindigoginmu a shekarar 2018, biyo bayan alkawarin da gwamnatin jihar ta yi na yin afuwa da sasantawa, babu wani abu da ya zo aljihun mu” inji shi.
“Mun halarci wasu horaswa, Amma haryanzu bawani ci gaba kan lamarin, Gwamnatin jihar batayi abun da ya dace ba, Kuma ba mu ji dadi ba, Bai kamata suyi mana hakan ba”
KARANTA WANNAN LABARIN: Kullum da Aure na ke Kwana a Raina inji Adamar Kamaye
Da yake jawabi ga masu zanga-zangar, babban sakatare a ofishin tsaro na jihar, Dokta Alfred Mboto ya zargi gwamnatin tarayya da yin watsi da jihar Cross River a shirin yi wamasu laifi Afuwa na gwamnatin tarayya .
A wani labarin Kuma na daban.
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanya ranakun 29 da 30 ga watan Oktoba domin gudanar da jarabawar gwajin a (CBT) a wani bangare na daukar aikin ‘yan sanda a jihar, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sanda SP Gambo Isah ya bayyanawa manema labarai, a ranar Litinin, a Katsina.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “An shirya gudanar da jarabawar ne a ranakun 29 da 30 ga watan Oktoba, 2021, a Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da kuma Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina daga karfe 8 na safe zuwa 3 na rana.
“Masu takara su duba imel ɗin su don samun takardar gayyata, wurin da kuma lokacin jarrabawar.
Ga wadanda basu samun sakwannin imel ba, ana ba su shawarar su kai rahoto zuwa hedikwatar ‘yan sandan Katsina, don bincika sunayensu,” in ji sanarwar.