By Ishaq Dabai
Babban sufeton ‘yan sanda na kasa IGP, Usman Alkali Baba, ya yabawa jami’an sa da sauran hukumomin tsaro bisa kokarin da suke na tabbatar da tsaro a jihar Kwara.
Da yake zantawa da jami’an rundunar ‘yan sandan yayin ziyarar da ya kai Ilorin, babban birnin jihar a ranar Laraba, Baba ya umarci jami’an nasa dasu sake sadaukar da kan su ga tsarin aikin dan sanda tare da yin watsi da duk wani abu da zai iya lalata martabar rundunar, ” kuna nan kuna yin aikin dan san yawa abi doka, yawancin mu masu hidima ga al’umma dole ne mu fito daga wasu sassan ƙasar. Kusa ni ku ‘Yan sandan Najeriya ne, ba’ yan sandan jihar Kwara bane ko kuma ‘yan sandan Ilorin.
“Don haka, dole ne mu sadaukar da kanmu don yin abubuwa da yawa. Duk da haka, ina so in taya ku murna cewa jihar Kwara ita ce jihar da ta fi zaman lafiya idan aka kwatanta da wasu da yawa,” in ji Baba.
IGP ya sake bayyana cewa aikin ‘yan sanda na al’umma ya kasance aikin son rai da ake nufi ga mutanen dake da aikin yi amma kawai suna son mayar wa al’ummarsu ta hanyar taimakawa wajen kiyaye lafiyar su.Bayanin ya zo ne bayan shawarwarin da ke nuna cewa gwamnati na shirin biyan wasu rukunin ‘yan sanda wadanda aka dauka kwanan nan a fadin kasar nan ciki har da na jihar Kwara.
Sannan ya bukaci jami’an ‘yan sanda a jihar da su ci gaba da jajircewa kan ayyukan su kuma su kasance masu da’a wajen yin hakan baya da haka rigunanku na iya sawa ku shiga aljanna ko wuta bisa la’akari da yadda suke gudanar da aikin ‘yan sanda.
Ya kara da cewa: “Lokacin da kuka sadaukar da kanku ga aikin ku na jami’in tabbatar da doka, kuna da ladan ku ba a iya nan kadai ba harma da sama domin hidimar zamantakewa ce. Wannan rigar zata ba ku aljannar ku kuma tana iya ba ku jahannama. Ya danganta da yadda kuke sawa da yadda kuke son yin aiki da shi. ”