Tumbukakken mataimakin gwamnan jihar Kogi, Simon Achuba, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya taimaka ya shiga tsakani domin kawo karshen rikita-rikitar siyasar da yake aukuwa a jihar, inda ya nemi da Buhari ya tabbatar da ganin an dawo da doka da oda a cikin jam’iyyarsa.
Achuba ya yi wannan kiran ne a garin Lokoja a ranar Lahadi jin kadan da kwashe kayansa daga gidan gwamnati da ya yi.
Achuba ya ce sanya bakin Buhari ne kawai zai kawo karshe matsalar da jam’iyyar APC take kokarin fadawa.