Cibiyar dake dakile cutuka masu yaduwa ta Nijeirya, NCDC a ranar Asabar ta bayyana cewa an kara samun mutum 1,598 da suka kamu da cutar korona a yayin da mutum bakwai suka rasu sakamakon cutar.
NCDC ta tabbatar da hakan ne a sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, inda ta ce yanzu wadanda cutar ta kama a Nijeriya sun kai 108,943, a yayin har yanzu akwai mutum 22,156 da ke dauke da cutar, inda kuma 1,420 suka warke daga cutar.
Rahotanni sun nuna cewa ya zuwa yanzu an yi wa ‘yan Nijeriya 1,147, 523 gwajin cutar ta korona tun bayan bullar cutar a Nijeriya a ranar 27 ga watan Fabarairun 2020.