Daga Mukhtar Yakubu
Fitaccen Mawakin Yabon Manzon Allah S A W Malam Bashir Dandago ya bayyana harkar Yabon Manzon Allah a wannan lokacin, da cewar ta shiga wani yanayin da ba a san Ina aka nufa ba.
Sha’irin ya bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin mu, Dangane da yanayin da harkar take ciki in da yake cewa:
“Ai tun da Hukumar tace finafinai ta kasa hada kan Sha’irai ina ganin a jira daga Allah kawai, domin hukumar ta gaza shiga ta yi wa kowa katin Shaida don tabbatar da shi, da kuma tafiya karkashin inuwa daya.
Ya kuma koka kan matsalar Jagoranci da suke fuskanta a tsakaninsu, inda yace idan aka dakko wani aka dora shi sai ya saka son zuciya, Saboda haka shi kuma shugaban Hukumar ya dauki abin da zafi, sai ya zama abin daga karshe ya yi shiru, don haka tun da Hukumar ta gaza to fa sai addu’a.”
Don haka sai ya yi Kira ga Sha’irai da cewar” su sani cewa harkar su ta Manzon Allah ce don haka a rinka ganin sa a aikace a wajen su, kamar yadda suke fadar Manzo to a gani a mu’amalar su, Amma ba a gan su suna yabo, kuma a gefe guda suna mu’amala da mutanan banza ba, ko bin mata.