Rahotanni daga gabashin Najeriya inda ake fama da kalubalen Yan Boko Haram, na bayyana cewar Yan BokoHaram din sun bindige wani matashin Soja a garin Bama.
Matashin Sojan mai suna Hussaini Adamu Musa da Yan kungiyar BokoHaram din suka hallaka sun bindige shi ne tun daga ranar Larabar data gabata.
Matashin yana da a kalla kimanin shekaru Ashirin da biyu kuma dan asalin Karamar hukumar Potiskum ne dake jihar Yobe.
Ya shiga gidan Soja tun a shekarar 2016,duk da dai bai dade sosai a gidan Soja ba, Hussaini ya taka muhimmiyar Rawa a gidan Soji musamman ta bangaren yakar yan Kungiyar BokoHaram.
Muna roko Allah ya gafarta mishi.