Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ya siffata gwamnatin APC karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a matsayin gwamnati mafi adalci tun zamanin mulkin mallaka a 1914.
Ya jawo shankalin sauran Yan Najeriya kan rashin yima gwamnatin Muhammadu Buhari fahimta mai kyau, yace ma Yan Najeriya suyi dubi da yanayin tattalin arziqin kasar nan yake duba da yadda farshin Mai yaje kasa tun karbar mulkin Buhari a 2015.
Yayi wannan bayani ne lokacin da ake kaddamar da tsarin ciyar da dalibai a jahar. Yace ya kamata mutane su gode a wannan lokacin gwamnatin, wadda ta kawoma al’umma cigaba a fannoni da dama.
KARANTA:- Laurette Onochie: Gwamnan Rivers ya zargi Jam’iyyar APC da nufin shirin murde zaben 2023 mai zuwa
Gwamnan ya buga misali da hidimar ciyar da dalibai da gwamnatin tarayya keyi da kuma sauran wasu tsarika na tallafi da gwamnatin ta kawo wanda anyi amfani da biliyoyin kudaden domin al’ummar kasa.
Nawa gwamnati take biya akan tsarin takkafin, ciyar da dalibai da gwamnatin tarayya take yi ya sanya yara da yawa an saka su makarantu, mutane suna magana ba tare da la’akari da kokarin da gwamnatin tayi ba. Kamar yadda Jaridar Leadership ta ruwaito a shafinta
“Koda kunki ko kunso gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta sanya talakawa wadanda basu san meye gwamnati ba sun sani, kuma sun ci moriyar ta.”
“Duk da matsalolin da shugaban Kasa yake fuskanta na karyewar farashin man fetur, da akwai lokacin da yakai rabbin rabi kan yadda ake sayar da shi a shekarar 2011 zuwa 2014.”
“In da badan hikima ta Dan adam ba, da sai mun tozarta, to amma ba muyi hakan ba, sai dai kawai muka dan canza kadan.”
Gwamnan ya nuna farin cikinsa da samar da tsarukan wanda mutane da dama sun amfana da haka, ya kuma samar ma wadansu aikinyi.
Sadiya Faruk Umar, Ministan Jinkai cewa tayi “kimanin milyan tara na yara ke cin moriyar abinci da ake rabawa a makarantu a kowace rana.”
“Yanzu munada burin kara Yara miliyan biyar izuwa shekarar 2023 kamar yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bada umarni.”