Tun Yanzu PDP ta amince da shan Kaye, ba tada abinda zata gayawa Ƴan Najeriya — Ministan Buhari
Ƙaramin Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyukan yi Festus Keyamo a ranar Asabar, ya ƙalubalanci Jam’iyyar PDP data karɓi shan Kaye Gabanin Babban Zaɓen Shekarar 2023.
Keyamo yace PDP na neman komawa Mulki ko ta halin wacce hanya.
Yana maida martani ne akan Ƙarar da PDP ta shigar, inda take neman Kotu ta haramta Babban Taron Jam’iyyar APC na Ƙasa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu ta kori ƙarar da gwamnoni su ka shigar da Gwamnatin Tarayya kan $418m na Paris Club
Ministan ya shawarci Babbar Jam’iyyar Hamayya data shirya yadda zata yiwa Ƴan Najeriya akan miyasa APC ta yiwa mutane ɗumbin ayyuka duk da ƙarancin Tattalin Arziki.
A jawabin daya rubuta, Keyamo yace “alamu sun nuna tuni Jam’iyyar ta karɓi shan kaye, kuma tana neman hanyar da zata koma kan Mulki.
“PDP ta shirya yiwa ƴan Najeriya jawabi a Babban Zaɓe tare da yi masu jawabi akan yadda a shekaru 7 (da ƙarancin Kuɗaɗe) tayi aiki fiye dana PDP na Shekaru 16.
Babbar Jam’iyyar Hamayya ta shigar da Ƙara, inda take neman APC ta haramta Babban Taron APC na Ƙasa.
A takardar shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CR/ 389/2022, Babbar Jam’iyyar Hamayya ta buƙaci Kotu ta hana Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta da amsar duk wani abu daya shafi Jam’iyyar APC.
Comments 1