Daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Janairun shekarar 1966, wasu kananan hafsoshin soja masu mukaman manjo sun aiwatar da juyin mulkin soja na farko wanda suka fara kitsawa tun a watan Agustar shekarar 1965.
Wadannan kananan hafsoshin soja, sun yi ikirarin cewa sun shirya juyin mulkin ne a saboda a cewarsu, shugabannin dake jagorancin kasar sun nuna zamiya, inda suka ce ministocin gwamnati suna sace kudaden baitul-mali domin amfaninsu.
Sai dai kuma a wani bangare, akwai masu ikirarin cewa wannan juyin mulki na kabilanci ne a saboda daga cikin sojoji 8 da suka kulla wannan juyin mulki, guda 7 ‘yan kabilar Igbo ne, daya kuma Bayarbe. A wani gefen kuwa, dukkan manyan shugabannin farar hular da aka kashe, har ma da wasu manyan hafsoshin soja, kusan ‘yan Arewacin Najeriya ne.
Wadanda suka shirya juyin mulkin, sune Manjo Chukwuma Nzeogwu wanda ke Kaduna a lokacin, wanda kuma shi ya jagoranci kashe Firimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto.
Manjo Emmanuel Ifeajuna, shine ya jagoranci juyin mulkin daga Lagos, kuma ya jagoranci kashe Firayim Minista Sir Abubakar Tafawa Balewa, da Birgediya Zakari Maimalari, wanda a lokacin shine hafsan soja mafi girma daga yankin Arewacin Najeriya.
Shugaban Kasa maras iko a lokacin, kuma dan kabilar Igbo, Nnamdi Azikiwe, ya bar kasar a lokacin da wadannan sojoji suka kaddamar da juyin mulkin.
A saboda Azikiwe ba ya cikin kasar, kuma an kashe firayim minista, sai mai rikon mukamin shugaban kasa a lokacin, Nwafor Orizu, shi ma dan kabilar Igbo, yayi jawabi ga kasa inda yace majalisar zartaswa ta yarda domin radin kanta, ta mika mulki ga sojoji.
Za mu Ci gaba.