Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta a ranar Alhamis yace zata yi amfani da kayayyakin zamani a lokacin watsa sakamakon Babban Zaben Shekarar 2023.
Hukumar tace akwai yiwuwar ta ɗauke muhimman kayayyakin ta daga Babban Bankin Najeriya zuwa wani wuri na daban.
KARANTA WANNAN LABARIN:Amurka tana Juyayi kan mutuwar Ƴan Ƙasar ta Miliyan 1 daga Cutar Covid-19
Shugaban Hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka a lokacin da yake wani taro da Kafafen Yaɗa Labaru a Abuja a ranar Alhamis.
Jaridar Dimokuraɗiyya tace Dayake maida jawabi akan tambayar da aka yi mashi ta ƙudirin Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele na Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa, Yakubu yace wannan ƙila ya sanya dole Hukumar ta canja wa muhimman kayayyakin ta wurin ajiya.
Shugaban Hukumar yace CBN ita ke da alhakin ɓoye dukkanin muhimman kayayyakin zaɓe, kuma Hukumar bata taɓa kokwanto wannan aikin Babban Banki.
Comments 1