Shugaba Kais Saied na Tunisia ya sanar da nadin Najla Bouden matsayin Firaminista wadda za ta zamo mace ta farko a tarihin kasar da za ta hau wannan kujera dai dai lokacin da shugaban ke ci gaba da fuskantar boren al’umma.
Wata sanarwa da ofishin shugaba Kais Saied ya wallafa a shafinsa na Facebook da ke sanar da nadin Najla Bouden a matsayin Firaministar ya kuma bukace ta da ta gaggauta kafa gwamnati don shawo kan matsalolin da kasar ta fada.
Nadin na Najla Bouden na zuwa bayan da shugaba Kais ya rushe gwamnatin Hichem Machichi a ranar 25 ga watan Yuli baya ga dakatar da majalisar kasar tare da karawa kansa karfin iko wanda ya tunzura al’ummar kasar.
Tuni dai zanga-zanga ta zafafa a sassan kasar ta Tunisia don kalubalantar matakin shugaban na dakatar da kundin tsarin mulki tare da kwace iko da bangaren shari’a.
Sakon bidiyon da Ofishin na Kais Saied ya saki a Facebook ya nuno shugaban tare da Firaminista Bouden lokacin da ya ke bayyana mata bukatar ganin ta tabbatar da kafa gwamnatin nan da sa’o’I ko kuma kwanaki masu zuwa.
PUBLICITÉ
Shugaban a jawabinsa bayan nadin, y ace matakin da ya dauka girmamawa ce ga matan kasar dama daukacin al’ummar kasar wadda ke fatan samar da daidaito tsakanin al’umma.
Bouden za ta zama Firaministar Tunisia ta 10 tun bayan hambarar da gwamnatin Zine El Abedine Ben Ali yayin juyin-juya halin kasar a 2011.
Najla Bouden, mai shekaru 63 wadda masaniyar ilimin albarkatun karkashin kasa ce ta rike mukamin daraktar hukumar ilimin kasar gabanin zama mamba a hukumar kula da ilimi mai zurfi.