An kori kocin Tunisiya Mondher Kebaier a ranar Lahadi, washegarin da kungiyarsa ta buga wasa da Burkina Faso a gasar cin kofin nahiyar Afirka da suka yii.
Hukumar kwallon kafar Tunisia ta tabbatar da cewa Kebaier, mai shekaru 51, wanda ya fara aiki tun watan Agustan 2019, za a maye gurbinsa da mataimakin kocinsa Jalel Kadri mai shekaru 50.
Tunisiya mai rike da kofin nahiyar Afirka a shekarar 2004 ta sha kashi da ci 1-0 a hannun Burkina Faso a ranar Asabar.
A wani labarin Kuma na daban
.
Zargi Cin Zarafi: Man United ta Dakatar da Greenwood Har Sai Baba Ya Gani
Dan wasa Mason Greewood ba zai bugawa Kungiyar Manchester United Wasa ba, ko halartar wajan Horaswanta , har sai baba ya gani, Kamar yadda kungiyar dake Kasar Burtaniya ta bayyana a yammacin yau Lahadi.
United ta bayyana hanakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar, bayan Jami’an Yan sandan Burtaniya sun sanar da gaiyatar Greenwood domin amsa wasu tambayoyi kan zargin da wata Budurwa ta shigar kan sa.
Tun da sanyin safiyar yau Lahadi ce dai, a ka wallafa Wani baifan bidiyo, da hotuna tare da Muryar budurwar a shafin ta na Instagram, inda take zargin Dan wasan da keta mata haddi, Wanda daga bisani aka goge sakon da aka wallafa.
Sanarwar da United ta fitar tun da farko, ta ce, “Mun Sami labarin abun da ya faru game da zarge-zargen da kenyawo a Kafafen sada zumunta na zamani, ba zamu ce komai ba har sai gaskiya ta bayyana, domin kuwa Manchester United bazata lamunci kowani irin rashin da’a ba”
Sai da kuma a sanarwa na biyu da Kungiyar ta fitar a yammacin yau Lahadi, ta bayyana matsayar Greenwood a kungiyar a halin yanzu, inda ta ce, ” Dan wasa Mason Greenwood ba zai bugawa Kungiyar wasa ba, Kuma ba zai halarci wajan Horaswanta ba, har sai baba ya gani”
A nashi bangaren Mai magana da yawun rundunar Yan sandan Yankin Manchester kamar yadda kungiyar Kafafen yada labarai ta Burtaniya ta ruwaito ya ce, ” Babu Shakka rundunar ta San da labarin hotuna da Faifan Bidiyon da suke yawo a Kafafen sada zumunta na zamani”
” Muna cigaba da bincike domin sanin cikakken abun da ya faru” inji shi