Rahotanni daga karamar hukumar Daura ta jihar Katsina na bayyana cewar masu garkuwa sun tafka babbar barna yau a garin.
Masu garkuwan sun yi dirar mikiya ne yau laraba bayan sallar magariba, inda suka sace Magajin Garin Daura, Musa Umar, a gidan sa dake daura.
Majiyar mu ta bayyana cewar Alhaji Musa Umar, tsohon shugaban hukumar fasa kauri ne Kwastam.
Rahotanni sun tabbatar da cewar Wanda aka sacen shine mahaifin Fatima Musa, matar Dogarin Shugaban kasa Muhammad Buhari, ADC Mohammed Abubakar.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewar, a lokacin da masu garkuwan suka yi dirar mikiyar, sun shiga garin da ruwan harsashi a wata mota kirar Fijo 406, wanda hakan ya basu damar yin awon gaba da Musa.