Dan tafka mahawara tare da baje kolin raayoyi game da batun tun bayan da mai temakawa Kwamishinan Yansandan Jihar Yobe, ya tabbatar da haka a lokacin da yake tattanawa da manema labaru.
Ya ce hukumar Yansanda Jihar Yobe ta dakume wani magidanci mai suna Muhammadu Hassan, bayan ta zarge shi da dirkawa Yar’sa ciki.
A lokaci da yake bayani a babban birnin jihar Yobe, Damaturu, matemakin Hukumar Yansandan ya ce yar tasa zata kai kimanin shekaru Ashirin da daya zuwa da biyu.
Bayanai sun bayyana cewar mahaifin Yarinyar Muhammad Hassan ya sadu da ita ne kawai su uku lokaci bayan lokaci, bayan ya jibga mata kayan maye.
Har ila yau rahotan ya laburta mana cewar Ciki dai ya kai kusan watanni biyar, a lissafi saura watanni hudu a haifi sabon bebi.