Shugaba kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana illolin da ke tattare da kau da kai, daga rikicin Habasha, da ya tilasta wa dubbai tserewa daga gidajensu.
Shugaban na Turkiyya, ya yi tayin shiga tsakani bangarorin biyu, domin tattauna mafita daga fadan da ake a tsakanin rundunar gwamnatin Habasha, da yan Kungiyar TPLF na yankin Tigray.
Erdoghan ya ce, yana da mahinmanci a dauki matakin shawo kan rikicin, domin ceto kasar daga durkushewa, ya kara da cewa, rikicin zai iya yin munmunan illa ga sauran kasashen yankin, idan aka ci gaba da zura ido ba tare da an dauki wani kwakwaran matakin dakatar da fadan ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kaduna ta fara saka ranar bude Makarantu
Ya dai fadi hakan ne a yayin wata ganawa da manema labarai da ya yi da Firaiministan Abiy Ahmed, da yanzu haka ke ziyarar aiki a kasar ta Turkiyya. Babu dai karin bayani kan cimma wata matsaya kan batun tattauna war, da shugaba Erdogan.
Tun dai a watan Nuwambar bara, fada ya barke a Habasha, dubban dubata sun tsere daga kasar, a ya yin da wasu sama da dubu dari hudu, ke fuskantar barazanar matsananciyar yunwa inji Majalisar Dinkin Duniya.
Comments 1