By Abbas Yakubu Yaura
Hukumomin kasar Turkiyya a ranar Talatar sun cafke wani mutum da ake zargi da hannu a cikin kisan shugaban kasar Haiti Jovenel Moise.
Kamfanin dillancin labaran kasar Anadolu ya bayar da rahoton cewa, Samir Handal, yana daya daga cikin wadanda ake zargi da kisan Moise a watan Yuli, an tsare shi a lokacin daya isa filin jirgin saman Istanbul.
Ya taso ne daga kasar Amurka. Rahoton ya kara da cewa an nemi Handal a kasar Jordan da kuma wucewa ta birnin Istanbul, inda ya kara da cewa an nemi Handal bisa sanarwar ‘yan sandan kasa da kada.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa an dai tura wanda ake zargin zuwa gidan yari a Istanbul bayan hukumomin kasar sun ba da umarnin tsare shi na wucin gadi na tsawon kwanaki 40.
Ministan harkokin wajen kasar Haiti Claude Joseph ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa ya tattauna da takwaransa na Turkiyya Mevlut Cavusoglu game da kamen ba tare da bayar da karin bayani ba.