Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya ce kasarsa a shirye take don kawo karshen yakin da ake gwabzawa, tsakanin Rasha da Ukraine, ta hanyar tattaunawar Dipomasiyya.
Ya bayyana cewa, ‘za mu ci gaba da bayar da gudunmuwa wajen magance yakin ta hanyar tattaunawar diflomasiyya.
Erdoğan ya shaidawa manema labarai a Turkiyya cewa tuni ya mika katin gayyatar tattaunawar ga shugaban kasar Ukraine din, yayin da yake ziyarar yini guda a Kasar.
Erdoğan da Zelenskyy da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres sun hallara a birnin Lviv na kasar Ukraine domin tattaunawa kan matakan kawo karshen yakin Ukraine da Rasha ta hanyar diflomasiyya da kuma kiyaye tsarin da aka kafa kwanan nan na fitar da hatsin Ukraine zuwa kasuwannin duniya.
“Mun kuma yi la’akari da yuwuwar canza yanayin da aka cimma da yarjejeniyar Istanbul zuwa zaman lafiya na dindindin,” in ji Erdoğan.
Erdoğan ya ce, Turkiyya, da Ukraine da Majalisar Dinkin Duniya sun tattauna kan matakan da za a iya dauka na fitar da hatsin da ake yi a Ukraine, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su dauki nauyin farfado da harkokin diflomasiyya.
A ranar 22 ga watan Yuli ne Turkiyya, Majalisar Dinkin Duniya, Rasha da Ukraine suka sanya hannu a kan yarjejeniyar bude tashoshin jiragen ruwa na tekun Black Sea guda uku na Ukraine don fitar da hatsin Ukraine da ya makale sakamakon yakin, wanda yanzu ke cikin wata na shida.
Erdoğan ya ce ya gana daban-daban da Zelenskyy da Putin tun lokacin da aka fara yakin, inda ya kara da cewa Turkiyya za ta gabatar da wannan batu a zauren Majalisar Dinkin Duniya a watan Satumba.