Sanata Uba Sani Ya Ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen sa, waɗanda zasu jagoranci yaƙin neman zaben sa a Takarar Gwamnan Jahar Kaduna daya ke yi a halin yanzu.
Sanata Uba sani Mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattijan Najeriya, kuma Ɗan Takarar Gwamnan jihar kaduna na cigaba da shirye-shirye a ƙoƙarin sa na Zama Gwamnan Jihar Kaduna, a jiya ya kaddamar da Kwamitin gudanarwa yakin Naman zabensa na 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gobarar Haramtacciyar Matatar Mai: An gano gawarwaki 109, wasu kuma sun bace bat a Imo
Sanatan ya bayyana haka a shafin sa na Twitter, inda ya bayyana Cewa ya ƙaddamar da kwamitin gudanarwa na takarar Gwamna, Kwamitin gudanarwa Wanda zai kasance ƙarƙashin Jagorancin Farfesa Muhammad Sani (Mainan Zazzau), a yayinda Hon Benjamin Jock zai zama Sakatare.
Kwamitin Mai ɗauke da mambobi arba’in da biyar 45, ya ƙunshi Shugabanni 23 da ke wakiltar kowace ƙaramar hukuma daga Cikin ashirin da uku 23 na Jihar kaduna da sauran 24 da aka zabo daga shiyoyin Sanata 3 na jihar Kaduna.
Kwamitin Gudanarwa zai samar da manufofi da dabarun tsarin takarar zama Gwamna na Sanata Uba Sani, da kuma yin salo da aiwatar da ingantattun dabaru don tabbatar da nasara a cikin tsarin tsayawa takara da kuma zaɓen na gwamna Mai Zuwa.
Manyan mutanen da suka halarci bikin ƙaddamar da Kwamitin sun haɗa da shugaban kwamitin majalisar wakilai na jihar Kaduna Rt. Hon. Tajudeen Abbas (Iyan Zazzau Dake wakiltar Zaria, Hon. Ahmed Munnir dake wakiltar Lere, Hon. Ibrahim Hamza PhD dake wakiltar Mazabar soba, Hon. Hamisu Kubau PhD dake wakiltar (Ikara/Kubau, Hon. Mukhtar Ladan dakw wakiltar Makarfi da Kudan sai kuma Hon. Mukhtar Zakari Dake wakiltar Kauru.
Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kaduna, Hon. Ahmed Mohammed Zaria Kewaye, Hon Auwalu Yaro Maikyau, Hon. Yusuf Dahiru (Mazabar Liman Makera),
Shuwagabannin ƙananan hukumomin da suka jagoranci bikin kaddamar da shugaban kungiyar ALGON reshen jihar Kaduna sun hada da Hon. Abubakar Buba (Lere LG Council). Sauran Shugabannin da suka shaida taron sun hada da Hon. Shuaibu Bawa Jaja (Kudan LG Council), Hon. Bashir S Zuntu (Kubau LG Council), Hon. Sadeeq Salisu (Ikara LG Council), Hon. Mukhtar Balony (Kaduna North LG Council), Hon. Haruna Bako (Kachia LG Council), Hon Bashir Dawaki (Kauru LG Council), Hon. Yunana Markus Barde (Jema’a LG Council), Hon. Abubakar Shehu (Giwa LG Council), Engr. Aliyu Idris (Zaria LG Council), Hon. Kabiru Jarimi (Kaduna South LGA Council), da Engr. Mohammad Usman Magu (Sabon Gari LG Council).
Haka kuma taron ya samu halartar tsaffin ‘yan majalisar wakilai, wato Hon. Abubakar Mamadi, Hon. Ibrahim Zero, Hon. Kabir Umar, Hon. Abdulkadir Global da Hon. Ruth Ango. Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Rt. Hon. Aminu Abdulfatah shi ma ya halarci taron, da kuma Charity Shekari, matar marigayi mataimakin gwamnan jihar Kaduna, H.E. Steven Shekara.
Sanata Uba sani na cigaba da Samun kwarjini Mai dauke da nuna goyon bayan Al’ummar Jihar kaduna.
Comments 1