Uba Sani Ya Jagoranci Tantace Mutanen Da Buhari Ya Turo Domin Basu muƙami a CBN
Sanata Uba Sani, Shugaban kwamitin Bankuna Inshora da Sauran Harkokin kuɗi, ya jagoranci tantance mutanen da Shugaban Ƙasa ya naɗa domin tantance su a matsayin Shuwagabannin Gudanarwar Babban Bankin Najeriya.
Sanata Uba Sani ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa daya fitar inda yace “A yau ne Kwamitin Majalisar Dattawa mai Kula da Harkokin Banki, Inshora da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi da nake shugabanta, ya tantance wadanda Shugaban Ƙasa ya nada domin a matsayin shugabannin gudanarwa na babban bankin Najeriya CBN.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ku daina yaudarar Ƴan Najeriya, ba Cigaban da Tinubu ya kawo a Legas – Jigon APC
Daraktoci hudu da aka sake naɗa su, wadanda ba na zartarwa bane sun haɗa da; Farfesa Mike Idiahi Obadan, Farfesa Justitia Odinakachukwu Nnabuko, Farfesa Ummu Ahmed Jalingo da Mista Adeola Adetunji.
A lokacin tantance su, an yi wa wadanda aka nada tambayoyi da dama kan wa’adin bankin na CBN, ƙalubalen da yake fuskanta, halin da ake ciki a bangaren banki da na hada-hadar kudi, yadda za a samar da hadin gwiwa mai karfi tsakanin hukumomin kudi da yadda za a fitar da Najeriya daga matsalolin tattalin arzikin da take ciki a yanzu.
A lokacin da Kwamitin ke Tantace su, waɗanda aka nada sun baje kolin fahimtar su akan tattalin arzikin Najeriya da kuma kalubale da sarkakiya, da damammakin bangaren hada-hadar kudi na Najeriya.
A lokacin zaman, Sanata Uba Sani, ya ƙi karɓar koke koke game da ɗaya daga cikin waɗanda aka zaɓa ba, wanda ya gabatar a gaban Kwamitin.
A madadin Kwamitin, Sanata Uba Sani ya bayyana godiyarsa ga Majalisar Dattawa bisa wannan damar da suka samu na yin wannan aiki, domin cigaban Najeriya.
Sanata Uba Sani shine Sanatan dake wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattijan Najeriya, kuma a halin yanzu shine Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Kaduna ƙarƙashin Jam’iyar APC.