• Andy Nnamdi Uba ya lashe zaben fidda Gwamni na jam’iyar APC a jihar Anambra.
• Zaben gwamnan jihar, zai gudanar ne a ranar shida ga watan Nuwanban shekaran nan.
• Shugaban kwamitin zaben fidda gwani na jam’iyar APC a jiharne ya bayyana shi a mastayin wanda ya lashe zaben.
Dan takarar kujerar gwamnan jihar Anambra karkashin Inuwar jam’iyar APC Andy Nnamdi Uba, ya doke abokan karawarshi guda 13, a zaben fidda gwani da jami’ar ta gudanar gabanin zaben gwamnan jihar a ranar 6 ga watan Nuwanban shekarar nan da muke ciki.
Shugaban kwamitin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyar APC a jihar, Kuma gwamnan jihar Ogun Prince Dapo Abiodun ne, ya bayyana shi a matsayin Wanda ya lashe zaben fidda gwanin, da ya gudana a Otal din Agulu Lake, da sanyin safiyar yau Lahadi.
Uba ya lashe zaben fidda gwanin ne da kiri’u 230,201 daga cikin kuri’un da aka kada a zaben.
Ga kadan daga ciki. jadawalin zaben:
i. Senator Andy Uba – 230, 201
ii. Dr. Chidozie Nwankwo – 21, 281
iii. George Moghalu – 18,596
iv. Paul Orajiaka – 4, 348
v. Geoff Onyejeagbu – 3, 414
vi. Azuka Okwuosa – 17,189
vii. Nwokafor Daniel – 3,335
viii. Ikoobasi Mokelu – 3,727
ix. Kwebuike Ifeanyi – 1,466
Kwamitin zaben fidda gwanin dai na jam’iyar APC ta yi amfani da tsarin nan ne da ke cewa, Karo bayan Kato.
.