Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya yi kira da a kara saka hannun jari da tallafa wa ilmin fasaha da na zamani, domin wadata matasa da dabarun da ake bukata don cigaba da yin gogayya a fannin tattalin arzikin duniya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a Sokoto yayin bikin mika makarantar ta Universal Basic Education Model Smart School ga gwamnatin jihar.
Gwamna Tambuwal ya ce, wurin ilimi wajen samun cigaban kasa da kawo sauyi ba za a mayar da shi baya ba.
Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa tana gina makarantu masu waya na Model guda talatin da bakwai a fadin kasar nan.
Manufar ita ce ba da fifiko ga ilimin zamani da fasaha don samun cigaban zamantakewa ta hanyar ilimin fasaha da na zamani don ba matasa kayan aiki da sanya su gasa.
Makarantar model smart da ke Sokoto ita ce ta farko da aka fara aiki a cikin guda talatin da bakwai a fadin kasar kuma jami’ai sun ce ana sa ran fara cikakken ayyukan ilimi a cikin wannan shekara.