Tsohon dan wasan kasar Ingila, Rio Ferdinand ya ce kocin Manchester City, Pep Guardiola ya shaida masa cewa kungiyarsa za ta doke Real Madrid a wasan kusa da na karshe.
Guardiola ya shaida mani cewa kungiyarsa za ta doke Spain kamar yadda suka yi shekaru biyu da suka gabata.
City ta lallasa Los Blancos da ci 4 da nema a filin wasa na Etihad.
Tsohon dan wasan kasar Ingila, Rio Ferdinand ya ce kocin Manchester City, Pep Guardiola ya shaida masa ta hanyar sakon kartakwana cewa kungiyarsa za ta doke Real Madrid kafin karawarsu ta kusa da ta karshe na gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Laraba kamar ya Daily Post ta rawaito.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa City ta lallasa Los Blancos da ci 4 da nema a filin wasa na Etihad, sakamakon kwallayen da Bernardo Silva ya ci da kuma kwallayen da Manuel Akanji da Julián Álvarez suka ci.
KARANTA WANNAN LABARIN: Maye Gurbin Messi: PSG Na Yunkurin Raba Arsenal Da Babban dan Wasanta
City dai na bukatar nasarar ne domin tabbatar da wasan karshe a karo na biyu a jere, kuma sun yi hakan ne da darasi domin ci gaba da fatan da suke da shi a gasar.
Da yake mayar da martani, Ferdinand ya ce Guardiola ya shaida masa cewa kungiyarsa za ta doke Spain kamar yadda suka yi shekaru biyu da suka gabata.
“Pep Guardiola ya aiko min da sakon waya kafin wasan yana mai cewa, ‘Ku yarda mun doke su kamar shekaru biyu da suka wuce, za mu sake doke su’,” kamar yadda BT Sports ta ruwaito.
A wani labarin kuma, Messi Ya Mayar Da Martani Yayin Da dan Wasan Barcelona Zai Bar Kungiyar
Shahararren dan wasan Barcelona, Lionel Messi ya mayar da martani ga ficewar kyaftin din kungiyar Sergio Busquets daga kungiyar ta Catalonia.
A baya dai Barcelona ta sanar da barin Busquets da kungiyar.
Busquets, tsohon dan wasan kungiyar, zai bar Barcelona a matsayin dan wasa a karshen kakar wasa ta bana, bayan ya shafe shekaru 18 a Blaugrana.
Da yake mayar da martani, Messi, a wani sakon Twitter da ya wallafa ta shafinsa na Instagram a ranar Laraba, ya yi fatan samun nasara ga Busquets a sabon matakin nasa.