Hukumar lafiya ta duniya ta ce an samu sabbin mutane shida da suka kamu da cutar Ebola a kasar Uganda a ranar Alhamis din nan, bayan da kasar ta ba da rahoton mace-mace ta farko daga cutar mai saurin yaduwa tun shekarar 2019.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Ma’aikatar lafiya ta Uganda ta sanar da barkewar cutar Ebola a gundumar Mubende da ke tsakiyar kasar a ranar Talata, inda ta sanar da mutuwar wani mutum guda mai shekaru 24.
A cikin wata sanarwa da WHO ta fitar, ta ce, “Ya zuwa yanzu, an tabbatar da kamuwa da cutar ebola guda bakwai, ciki har da mutuwar mutum guda, wadanda suka kamu da cutar daga Sudan.”
KARANTA KUMA: Mutane Goma Sun Kamu Da Cutar Ebola
“An gano mutane arba’in da uku kuma mutane 10 da ake zargin sun kamu da kwayar cutar suna karbar magani a asibitin yankin da ke Mubende,” in ji ta.
Tashar talabijin ta Channels ta rawaito cewa, Abdou Salam Gueye, darektan gaggawa na yankin ofishin hukumar WHO na Afirka ya ce “Tuni kwararrun mu sun kasance a kasa suna aiki tare da kwararrun kungiyoyin yaki da cutar Ebola na Uganda don karfafa sa ido, tantancewa, jiyya, da matakan kariya.”
Uganda – wacce ke da iyaka da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (DRC) – ta fuskanci barkewar cutar Ebola da dama a baya, na baya-bayan nan a cikin shekarar 2019, lokacin da akalla mutane biyar suka mutu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai AFP ya rawaito.
A wani labarin kuma: 2023: ‘Yan Takarar Shugaban Kasa Za Su Sanya Hannu Kan Wata Yarjejeniya
Kwamitin wanzar da zaman lafiya na kasa (NPC) ya tsara ranar Alhamis mai zuwa ga ‘yan takarar shugaban kasa da su rattaba hannu kan yarjejeniyar ‘yanci, gaskiya da lumana, gabanin yakin neman zabe.
A watan Janairu, za su kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar amincewa da sakamakon zaben na 2023.