Shugaba Volodymyr Zelensky a ranar Talata ya ce Ukraine ta amince da cewa ba za ta zama mamba a kungiyar tsaro ta NATO ba.
Zelensky ya ce lokaci ya yi da Ukraine za ta yarda ba za ta shiga NATO ba.
“Ukraine ba memban NATO ba ce. Mun fahimci haka.
“Mun dade muna jin cewa kofofin a bude suke, amma kuma mun ji cewa ba za mu iya shiga ba. Gaskiya ce kuma dole ne a gane ta, “in ji Zelensky.
Shugaban na kasar Ukraine ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da shugabannin sojojin kasar a ranar Talata.
Yiwuwar shiga kungiyar tsaro ta NATO, kawancen soji da Amurka ke jagoranta, na daya daga cikin dalilan da suka sa Rasha ta fara kai hari kan Ukraine a watan Fabrairun shekarar nan.
Harin na Rasha ya zuwa yanzu ya haifar da rikicin ‘yan gudun hijira mafi girma a Turai tun bayan yakin duniya na biyu inda sama da mutum miliyan uku suka yi ta yin gudun hijira domin tsira da rayukansu ciki har da mata da kananan yara.