Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha a ranar Talata ta ce an hana shugaban Amurka Joe Biden da wasu manyan jami’an gwamnatin kasar goma shiga kasar a wani mataki na mayar da martani ga takunkumin da Amurka ta kakabawa Rashan.
Matakin, wanda kuma ya shafi sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da kuma sakataren tsaro Lloyd Austin, “sakamakon manufar nuna kyama ce ga gwamnatin Amurka ta yanzu”, in ji ma’aikatar harkokin wajen Rasha a cikin wata sanarwa da ta fitar dangane da na ta takunkumin.
Sai dai tun da fari, Dangane da katsalandan din sojan da Rasha ta yi a Ukraine, Amurka ta haramtawa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov shiga kasar ta, tare da daukar matakan kakabawa Rasha takunkumin da ya katse kudaden da Rasha ke samu daga sauran kasashen duniya.
Har ila yau Rasha ta saka sunayen shugaban hafsan hafsoshin sojan Amurka Mark Milley da mai ba da shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan da daraktan hukumar leken asirin kasar William Burns da kuma sakatariyar yada labaran fadar White House Jen Psaki.
Haka kuma a cikin jerin sunayen akwai mataimakin mai ba da shawara kan harkokin tsaro Daleep Singh, da shugabar hukumar raya kasashe ta Amurka Samantha Power, da mataimakin sakatariyar baitulmalin kasar Adewale Adeyemo, da shugabar bankin shigo da kayayyaki na Amurka Reta Jo Lewis.
Rasha ta kuma haramtawa dan Biden Hunter da tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka kuma Tsohuwar ‘yar takarar shugaban kasa ta jam’iyar Democrat Hillary Clinton shiga kasar tata.
Ma’aikatar Harkokin Wajen ta yi gargadin cewa nan ba da jimawa ba Moscow za ta ba da sanarwar karin takunkumi kan wasu jami’an gwamnatin Amurka, jami’an soji, ‘yan majalisa, manyan ‘yan kasuwar kasar , da kuma wasu kafofin yada labarai na kasar.