Majalisar dokokin Ukraine a ranar Laraba ta kafa dokar ta baci da nufin taimakawa wajen samar da martani ga barazanar mamayar Rasha.
An amince da matakin da gagarumin rinjaye a yau laraba da Moscow ta fara ficewa daga ofishin jakadancinta na Kyiv, kuma Washington ta kara yin gargadi game da yiwuwar kai hari ga Rasha.
Akwai Karin bayani……
A wani labarin Kuma na daban
Har yanzu dai ba a san inda wasu yara biyar da wata mata ta sace ba wanda ta yi kama da malamar koyar da darasin gida a unguwar Rukpakulusi da ke garin Eliozu a jihar Ribas kwanaki 11 da faruwar lamarin.
Yaran biyar masu shekaru tsakanin watanni 18 zuwa hudu, wadanda ake zargin ta sace su ne bayan da ta bukaci su biyo ta inda za ta saya musu kayan rubutu.
Mahaifin yaran biyu, Mista Emmanuel Benjamin, ya shaida wa jaridar PUNCH a ranar Talata cewa, ‘yan sanda a ofishin Okporo sun bukaci ya biya su kudi naira 200,000 domin a gaggauta yin bincike tare da gano wandanda ake zargin.
Emmanuel ya bayyana bakin cikinsa kan lamarin, inda ya ce bai san halin da yaran na sa da aka bayyana sunayensu da Idara da Emem ke ciki ba.
“Tun ranar ban ga ‘ya’yana ba. Ban ji dadi ba. Babu wanda bazai yi baƙin ciki ba idan irin haka ta same shi. Ba zan iya ko barci ba kuma ba na jin dadi ko kadan,” in ji shi.
Ya yi nuni da cewa ‘yan sanda sun bukaci iyalan dasu bada kudi domin a gaggauta yin bincike kan lamarin.
“Basa aiki akan wannan lamarin, Idan muka je sai suka ce mu kawo kudi.
“Na je ofishin ‘yan sanda na Okporo. Sai suka ce mu kawo kudi da lambar wayar da za su bibiyesu. Sai suka ce mu kawo Naira 200,000 don su nemo inda matar take zaune. Amma ba ni da irin wannan kuɗin. Ni ba babban mutum ba ne,” in ji Emmanuel.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, an kasa samun jin ta bakin kan lamarin.