Gwamnan Jahar Ebonyi Dave Umahi a ranar Juma’a ya sanar da dakatar da Kwamishinan Ƙasa da Sufiyo Chief Emmanuel Uguru sakamakon sakacin aiki.
Umahi ya kuma kori Mrs Obianuju Alo, Babban Mai Taimaka masa akan ilmi, shima akan sakaci da aiki.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jahar Dr. Kenneth Ugbala ya fitar ga Manema Labaru a Abakaliki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan tsaro ya ƙaryata batun naɗa sabon Darkta-Janar na Hukumar NIA
A cewar Sanarwar, Uguru da Alo zasu zauna a gida na tsawon watanni wata ɗaya, wanda dokar ta fara nan take.
“Kwamishinan Ƙasa da Sufiyo Chief Emmanuel Uguru da Babban Mai Taimaka masa akan ilmi Dr. Obianuju Alo, an umarce su dasu fara zaman wata ɗaya na dakatar dasu da aka yi.
Umahi a yau ta dakatar da Chief Emmanuel Obasi, Sakataren shi, sakamakon wasa da aiki.
Comments 1