Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa ya tattauna da Ummakulsum Buhari wadda aka fi sani da Ummita kan dangantakarta da dan kasar China da ya kashe ta a Kano.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda aka kashe matashiyar a unguwar Janbulo da ke karamar hukumar Gwale a jihar Kano a daren ranar Juma’a.
Malamin ya ce ta kira shi a waya domin neman shawararsa kan auren dan kasar China.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Daurawa ya ce a lokacin ya shaida mata cewa iyayenta sun fi ta gaskiya, domin rashin sanin asalin masoyinta mai suna Gheng Quanrong kafin aure yana da hadari.
KARANTA KUMA: Wani Dan China Ya Kashe Budurwarsa Mai Shekaru 23 A Kano
Malamin ya kara da cewa a dalilin haka ne ya gindaya mata sharudda biyar, inda ya ce ya tabbatar mata da cewa idan ta cika su da kan sa zai ci gaba da jan hankalin iyayenta su amince da auren.
Sharuɗɗan Daurawa sun haɗa da tuntuɓar Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (NIS) don tabbatar da sahihancin shigowar sa Nijeriya, inda yake aiki.
Har ila yau, Daurawa ya ce kasancewar Sarkin Kano ya nada shugaban yan kasar Sin a jihar zai zama mai sauki a gareta wajen bincike a kansa.
Ya ce sharadi na karshe da ya gindaya mata shi ne a sanar da hukumar Hisbah ta jihar Kano domin ta koya wa dan kasar Chana addinin Musulunci saboda an ce ya musulunta.
Daga karshe malamin ya ce ta amince ta bi shawararsa, inda ya tabbatar mata da zarar ta kammala su ba tare da wata matsala ba zai tuntubi iyayenta kan auren.
Sheikh Daurawa ya ci gaba da cewa addinin musulunci bai hana musulmi auren wani daga wata kabila ba matukar sun cika ka’idojin aure na addini.
A wani labarin kuma: Kotu Ta Kori Karar Da PDP Ta Shigar Kan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa Na APC Da LP
Mai shari’a Donatus Okorowo na babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Litinin din nan ya yi watsi da karar da jam’iyyar PDP ta shigar na neman a soke takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu da na jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi bisa zargin sauya abokan takarar su ba bisa ka’ida ba.
Alkalin ya ce PDP tana da nufin tada hankalin abokan hamayya a zaben shugaban kasa na 2023.