Asusun Tallafawa Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da Asusun hadaka domin bunkasa Fannin Ilima a fadin duniya tare da Gwamnatin Jihar Nasarawa, sun ce sun mayar da daliban da ba su zuwa makaranta guda 10,353 zuwa makaranta a kananan hukumomi biyu na jihar.
Jami’in kula da kananan yara na UNICEF a ma’aikatar ilimi, Mista Ali Musa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a garin Lafia, babban birnin jihar, a wani taron bita na duba rahoton ci gaban da aka samu daga aikin da aka yi a baya da kuma bayar da shawarwari kan ayyukan.
“A cikin makarantu 205 da ke Lafia da kuma makarantu 165 a karamar hukumar Nasarawa, an mayar da yara maza 6,116 da mata 4,237 makarantun a karkashin wannan aikin,” inji shi.
Ya kara da cewa, illar cutar korona da ke dagula tattalin arzikin kasashe da dama, ta janyo asarar ayyukan yi da iyaye ke yi, kuma yana daya daga cikin dalilan da suka sa yara suka daina zuwa makaranta a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sojoji Sun Tabbatarwa Buhari Sabuwar Dabarar Magance ‘Yan Bindiga Da ‘Yan ta’adda – NSA
Yayin da ya ke lura da cewa UNICEF ta fito da shirin komawa makaranta don taimakawa wajen dawo da wadanda suka daina karatu a sakamakon COVID-19 da wasu dalilai, ya ce a halin yanzu ana gudanar da aikin a fadin makarantun firamare 370 a kananan hukumomin Lafia da Nasarawa.
Tun da farko, kwamishiniyar ilimi da kimiyya da fasaha ta jihar, Fatu Sabo, wanda Daraktan tsare-tsare, bincike da kididdiga a ma’aikatar, Mista Abdulkareem Bala ya wakilta, ta bayyana cewa tun daga lokacin ne gwamnati ta sanya hannu kan wannan shiri na tabbatar da cewa duk wani yaron da aka haifa yazama wajibi akai shi makaranta idan shekarun zuwansa makaranta sun kai.
A wani labarin kuma na daban.
Chelsea ta cimma matsaya kan yarjejeniyar sirri da dan wasan bayan Leicester City Wesley Fofana, in ji Ignazio Genuardi.
Ana tunanin Chelsea na neman wani dan gwararran dan wasan baya bayan ta rasa siyan Jules Kounde, wanda ke shirin komawa Barcelona daga Sevilla a cikin kwanaki kadan masu zuwa.
Fofana dai ana alakanta shi da barin Leicester a kakar wasa ta bana kuma da alama yanzu Chelsea ta dauki matakin kawo shi Stamford Bridge.
Har yanzu Chelsea ba ta cimma matsaya kan farashin dan wasan ba tsakaninta da kungiyar Leicester, duk da haka, akwai yiwuwar Leicester City za ta bukaci kudi mai yawa domin ta bar Fofana kafin a fara sabon kakar wasa a watan Agusta mai kamawa.